Nov 08, 2018 11:48 UTC
  • Rasha Ta Bukaci Zaman Kwamitin Tsaron MDD Kan Korea Ta Arewa

Gwamnatin kasar Rasha ta bukaci kwamitin tsaro na MDD ya gudanar da taron sirri kan kasar Korea ta Arewa a wannan alhamis.

Kamfanin dillancin labaran Irna ya habarta cewa hukumomin birnin Mascow sun bukaci kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da taron sirri domin sassauta takunkumi a kasar korewa ta arewa, kuma wannan bukata na zuwa ne a yayin da aka dage ganawar da aka shirya yi tsakanin saktaren harakokin wajen Amurka Mike Pompeo da mataimakin Shugaban kasar Korea ta Arewa  Kim Yong-chol.

A daren jiya Laraba, Shugaban Amurka Donal Trump ya bayyana cewa ba zai sassauwa takunkumin da kasar ta kakabawa kasar Korewa ta kudun ba.

Saidai a makun da ya gabata, Shugaban kasar Korewa ta arewa ta sanar da cewa mtukar dai Amurka ba ta sassauta mata takunkumin da ta kakaba mata ba, to akwai yiyuwar ta ci gaba da shirinta na bunkasa makamanta na Nukiliya. 

Tags