Pars Today
Taho mu gama tsakanin dali'an jami'a da jami'an tsaron kasar Senegal ya yi sanadiyar mutuwar dalibi guda tare kuma da jikkata mutane 20 na daban.
Kungiyoyin bada agaji na majalisar dinkin duniya da wasu masu zaman kansu sun yi gargadi kan yiyuwan samun karancin abinci a yankin Sahel idan har daminar bana bata yi kyau ba.
'Yan sanda sun yi amfani da karfi wajen tarwatsa daruruwan masu zanga-zanga a birnin Dakar, babban birnin kasar Senegal wadanda suka fito don nuna rashin amincewarsu da kokarin da 'yan majalisar kasar suke yi na yin sauyi ga kundin tsarin zabe na kasar.
Kotu a kasar Senegal ta yanke hukuncin daurin shekaru 15 a kidan kaso kan ga wani dan kasar mai dauke da takardar zama dan kasar Faransa bayan da ta same shi da lafin alaka da kungiyoyin 'yan ta'adda.
Ministan harkokin harkokin waje na Jamhuriya Musulinci ta Iran, Muhammad Jawad Zarif, ya isa a birnin Dakar na kasar Senegal, a wani yunkuri na kara karfafa alakar dake tsakanin kasashen biyu.
Wata kotu a kasar Senegal ta zartar da hukuncin dauri na tsawon shekaru 15 a gidan kurkuku kan wani dan kasar da ke da takardar dan kasa a Faransa bayan samunsa da laifin shiga kungiyar ta'addanci.
A Senegal, lauyoyin magajin birnin Dakar, Khalifa Sall, sun sanar da cewa zasu daukaka kara kan hukuncin da kotun birnin ta yanke masa na shekaru biyar a gidan yari da kuma tarar miliyan biyar.
Kamfanin Dillancin labarin Waj na kasar Aljeriya da ya ba da labarin ya kara da cewa; Mutane 20 suka rasa rayukansu da kuma jikkata sanadiyyar hatsarin
'Yan sandan kasar ta Senegal sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa mutanen da suka amsa kiran jam'iyyun hamayya na yin Zanga-zanga.
'Yan sanda a birnin Dakar na Senegal na tsare da wasu jagororin 'yan adawa biyu, a yayin wata zanga-zanga da hukumomin kasar suka haramta.