Senegal : Lauyoyin Khalifa Sall Sun Daukaka Kara
A Senegal, lauyoyin magajin birnin Dakar, Khalifa Sall, sun sanar da cewa zasu daukaka kara kan hukuncin da kotun birnin ta yanke masa na shekaru biyar a gidan yari da kuma tarar miliyan biyar.
Daya daga cikin lauyoyin magajin birnin, Sheikh Khouraissi Bâ, ya ce zasu hada kai don kalubalantar hukuncin ta hanyar daukaka kara.
Saidai su ma lauyoyin gwamntin Senegal sun ce zasu daukaka kara akan duk abunda ya shafi kare dukiyar al'umma.
Tunda farko dai kotun ta bukaci hukuncin dauri na shekaru bakwai kan Khalifa Sall, da ake zargi da shi da wasu abokan aikinsa bakwai da karkata akalan kudade da yawansu ya kai Bilyan 1,83 na kudin CFA a tsakanin 2011 da 2015, koda yake daga baya kotun ta ce yawan kudaden Bilyan 1,65 ne CFA.