Feb 28, 2019 07:16 UTC
  • Ana Daf Da Sanar Da Sakamakon Zaben Shugaban Kasa A Senegal

Hukumar zabe mai zaman kanta a Senegal, ta sanarda cewa da ranar yau, Alhamis ne zata sanar da sakamakon zaben shugaban kasar da aka kada kuri'arsa a ranar Lahadi data gabata.

Hukumar ta kuma ja hankalin 'yan siyasar kasar akan wallafa duk wani sakamakon zabe, wanda ta ce ita ce kawai keda hurumin yin hakan.

Hakan dai na zuwa ne bayan da fira ministan kasar, ya sanar da wani sakamakon zabe a ranar Litin dake nuna cewa shugaban kasar mai neman wa'adi na biyu ne Macky Sall ya yi nasara a zaben, lamarin da ya tayar da kakkausan suka dagan bangaren 'yan adawan kasar.

Hukumar zaman kasar ta Senegal, ta ce 'yan takarar dake da korafi akan zaben suna da sa'o'i 72 domin gabatar da korafe korafensu gaban kotun tsarin mulkin kasar, wacce ita ce keda hurimin tabbatar da sakamakon zaben na din-dindin.

Kafin hakan dai kungiyoyin kasa da kasa dake suka sanya ido a zaben na Senegal, sun yada da yadda aka gudanar da zaben.

Tags