Ziyarar Ministan Harkokin Wajen Iran A Senegal
(last modified Tue, 10 Apr 2018 06:42:44 GMT )
Apr 10, 2018 06:42 UTC
  • Ziyarar Ministan Harkokin Wajen Iran A Senegal

Ministan harkokin harkokin waje na Jamhuriya Musulinci ta Iran, Muhammad Jawad Zarif, ya isa a birnin Dakar na kasar Senegal, a wani yunkuri na kara karfafa alakar dake tsakanin kasashen biyu.

Wannan dai na daga cikin ran gadin da Mista Zarif, ya fara a wasu kasashen Afrika da kuma na Latine Amurka.

A kasar ta Senegal inda ya fara ziyarar a jiya, ministan harkokin wajen kasar ta Iran, ya gana da takwaransa na Senegal Sidiki Kaba, kafin daga bisani ya gana da wasu manyan jami'an gwamnatin ta Senegal.

Tawagar da Zarif ke jagoranta ta kunshi 'yan kasuwa da kuma masu zuba jari, inda zasu tattauna kan hanyoyin bunkasa alaka da dangantaka da karfafa harkokin cinikaya da zuba jari tsakanin bangarorin biyu.

Bayan Senegal, ministan harkokin wajen ta Iran zai ziyarci kasashen Namibiya, Brazil da Uruguay.