Pars Today
Jami'an tsaron kasar Senegal sun damke wasu mutane biyu dukkanin 'yan kasar Mali da ake zargin suna da hannu a hare-haren ta'addancin a kasar Ivory Coast a cikin watan Mris 2016.
Kasashen Senegal da Gambiya sun tabbatar da karfafa alakar dake tsakanin su
Akalla mutane 170 'yan kasar Senegal da ke nufin tafiya ci rani zuwa kasashen turai ne aka mayar da su gida daga kasar Libya.
Shugaban kasar Gambia Adama Barrow ya bayyana cewa zai cire siffar muslunci daga cikin sunana kasar ta Gambia.
Ministan harkokin wajen kasar Senegal Mankeur Ndiaye ya bayyana cewar shugabannin kungiyar tattalin arzikin kasashen Yamamcin Afirka (ECOWAS) ba su amince da batun ba wa tsohon shugaban kasar Gambiya, Yahya Jammeh kariya ba.
Shugaban Ghana ya sanar da amincewar kasarsa kan aikewa da sojoji zuwa kasar Senegal domin shiga cikin sahun rundunar hadin gwiwa ta kungiyar bunkasa harkar tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS da zasu yi amfani da karfi wajen kawar da shugaba Yahaya Jamme'i daga kan karagar mulkin kasarsa.
Shugaban kasar Senegal Macky Sall ya amince da bukatar da takwarorinsa shugabannin kasashen Afirka suka gabatar masa na baiwa zababben shugaban kasar Gambiya Adama Barrow mafaka ta siyasa har sai an rantsar da shi a matsayin sabon shugaban kasar Gambiyan a ranar 19 ga watan nan na Janairu.
A sakonsa na shiga sabuwar shekara shugaban kasar Senegal ya karfafa aiki da hanya ta sulhu domin kawo karshen takaddamar siyasa a kasar Gambiya.
Kasar Senegal ta yi karin haske dangane da dalilan da ya sanya ta kada kuri'ar a kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya don dakatar da ci gaba da gine-ginen matsugunan yahudawa da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila take yi a yankunan Palastinawa.
Shugaban Gambia Ya yi amai ya lashe