Za A Cire Siffar Musulunci Daga Cikin Sunan Kasar Gambia
(last modified Mon, 30 Jan 2017 12:57:36 GMT )
Jan 30, 2017 12:57 UTC
  • Za A Cire Siffar Musulunci Daga Cikin Sunan Kasar Gambia

Shugaban kasar Gambia Adama Barrow ya bayyana cewa zai cire siffar muslunci daga cikin sunana kasar ta Gambia.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya nakalto daga shafin yada labarai na Sabil ya habarta cewa, a jawabinsa na farko a jiya bayan da ya shiga cikin kasar Gambia bayan ficewar Yahya Jammeh, Adama Barrow ya bayyana cewa zai canja sunan kasar.

Ya ce Yahya Jammeh tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar ya canja sunan kasar Gambia zuwa jamhuriyar musulunci domin ya wanke kansa daga barnar da yake aikatawa da sunan muslunci, ya ce wannan ya kawo karshe.

Adama Barrow bisa la'akari da cewa mafi yawan al'ummar kasar Gambia musulmi ne ba zai yiwu a cire al'adu da addinin muslunci daga harkokin jama'a na kasar ba, amma ba za a yi amfani da sunann muslunci domin cimma wasu manufofi na siyasa ba.

Tsohon shugaban kasar Gambia Yahya Jammmeh dai ya kwashe tsawon shekaru 22 yana mulkin kasar, inda ya sha kayi a zaben da aka gudanar a kasar a cikin watan Disamban shekarar da ta gabata.