Senegal ta jaddawa wajabcin Warware Rikicin kasar Gambiya Ta Ruwan Sanyi.
A sakonsa na shiga sabuwar shekara shugaban kasar Senegal ya karfafa aiki da hanya ta sulhu domin kawo karshen takaddamar siyasa a kasar Gambiya.
A sakonsa na shiga sabuwar shekara shugaban kasar Senegal ya karfafa aiki da hanya ta sulhu domin kawo karshen takaddamar siyasa a kasar Gambiya.
Macky Sall ya ci gaba da cewa; Kasarsa tana yin duk abinda za ta iya a fagen diplomasiyya da ya hada da zuwa kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya domin kawo karshen rikicin Gambiya.
Shugaban kasar Gambiya Yahya Jammeh wanda ya shekara fiye da 22 akan karagar mulki,ya janye amincewar da ya yi da sakamakon zaben da ya bai wa Adama Barrow nasarar lashe shi, bayan da a farko ya yi furuci da hakan.
Kungiyar tattalin arziki ta kasashen yammacin Afirka ta nada shugaban Najeriya,mai shiga tsakani domin warware takaddamar siyasar ta Gambiya.