Pars Today
Ma'aikatar lafiya a Palasdinu ta sanar da cewa: Palasdinawa 4 ne suka yi shahada yayin da wasu adadi mai yawa suka jikkata sakamakon hare-haren wuce gona da iri da jiragen saman yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai kan yankin Zirin Gaza.
A Ci gaba da zanga-zangar neman dawo da hakki, wani matashin Bapalastine ya yi shahada sanadiyar mumunar rauni da ya samu a jiya Juma'a
Majiyar tsaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sanar da cewa: Jami'an tsaron kan iyakar kasar guda biyu sun yi shahada a yankin Korin da ke garin Zahedan a shiyar kudu maso gabashin kasar.
Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun bude wuta kan tawagar Palasdinawa a shiyar gabashin yankin Zirin Gaza lamarin da ya janyo shahadar bapalasdine guda.
Dauki ba dadi tsakanin jami'an tsaron kan iyakar kasar Iran da wasu gungun 'yan bindiga masu fataucin muggan kwayoyi ya yi sanadiyyar shahadar jami'in tsaron Iran guda.
Ma'aikatar kiyon lafiyar Palastinu ta sanar da shahadar wani Bapalastine a yayin zanga-zangar Dawo Da Hakki.
Jami'an tsaron HK Isra'ila sun buda wuta kan wani gungun matasan Palastinawa a yankin kan iyaka da gabashin Khan Yunus, lamarin da ya yi sanadiyar shahadar biyu daga cikinsu.
Ana ci gaba da yin Allwadai da kisan gillar da kawancen Saudiyya da Amurka suka yi wa shugaban majalisar koli ta siyasa a kasar Yeman Saleh Sammad.
Wani bafalasdine da ya samu raunuka sakamakon harbinsa da bindiga da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suka yi a gabashin birnin Qudus ya yi shahada.
Da safiyar yau laraba ne sojojin Sahayoniya su ka harbe wani matashin Bapalasdine a arewacin al-Khalil da ke yammacin kogin jordan.