Wani Bafalasdine Ya Yi Shahada A Yankin Gabashin Birnin Qudus
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i29770-wani_bafalasdine_ya_yi_shahada_a_yankin_gabashin_birnin_qudus
Wani bafalasdine da ya samu raunuka sakamakon harbinsa da bindiga da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suka yi a gabashin birnin Qudus ya yi shahada.
(last modified 2018-08-22T11:31:40+00:00 )
Apr 09, 2018 18:54 UTC
  • Wani Bafalasdine Ya Yi Shahada A Yankin Gabashin Birnin Qudus

Wani bafalasdine da ya samu raunuka sakamakon harbinsa da bindiga da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suka yi a gabashin birnin Qudus ya yi shahada.

Majiyar Asibitin Palasdinu ta sanar da cewa: Matashin bafalasdine mai suna Muhammad Abdul-Karim Marshud dan shekaru 30 a duniya da ya samu raunuka sakamakon harbinsa da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suka yi a yankin birnin Qudus da aka mamaye ya yi shahada a yau Litinin.

A gefe guda kuma Cibiyar kare hakkin bil-Adama ta Palasdinu a yau Litinin ta fitar da sanarwar cewa: A cikin watan Maris da ta gabata gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta kame Palasdinawa 609 tare da tsare su a gidajen kurkuku.

Sanarwar ta kara da cewa: A cikin Palasdinawan da ake kame kuma ake ci gaba da tsare su 13 mata ne gami da kananan yara 95.