Feb 07, 2019 07:00 UTC
  • Kungiyar Hamas Ta Dora Alhakin Shahadar Bapalastine  A Gidan  Kurkukun Yahudawa Kan Sahayuna

Kungiyar gwagwarmayar Palastinawa (hamas) ta ce shahadar da Faris Barun ya yi a gidan kason yahudawa rashin kulawa ne na jami'an kiyon lafiyan gidan Kurkukun

Cikin wani jawabi da ta fitar a jiya Laraba, har ila yau kungiyar ta Hamas ta bukaci dukkanin al'ummar Palastinu kama daga kungiyoyin gwagwarmaya da na kare hakin bil-adama gami da na siyasa da su gaggauta daukan mataki na ceto dubun dubutan al'ummar Palastinu da ake tsare da su a cikin gidajen kurkuku na Sahayuna.

Kungiyar ta Hamas ta tabbatar da cewa irin wannan ta'addanci da ake aiwatar kan fursinonin Palastinawa ba zai yi sanadiyar raunana ci gaba da gwagwarmayar al'ummar kasar ba.

Har ila yau kungiyar ta ce jihadi da gwagwarmaya ita ce hanya daya cilo da za ta kawo karshen bala'in da fursinonin Palastinawa suke fuskanta a gidajen kurkukun Sahayuna.

Faris Barun da ya kasance mazaunin yankin zirin gaza na daga cikin fursunoni mafi jimawa a gidan kurkukun Sahayuna wanda ya yi shahada a jiya Laraba sakamakon rashin kulawar likitoci na gidan kurkukun.

Rahoton ya ce jim kadan bayan shahadar Faris Barun, an samu hatsaniya a gidajen kurkukun sahayunan, lamarin da ya sanya aka rufe gidajen kurkukun Nafha da Raimun.

Tags