Dec 07, 2018 04:15 UTC
  • Kudirin Amurka Na Yin Allawadai Da Hamas Ya Ki Karbuwa A MDD

Kudirin da Amurka ta gabatar na bukatar yin allawadai da kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas, ya kasa samun karbuwa a majalisar dinkin duniya.

Kudirin da jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Nikki Haley, ta gabatar ya samu kuri'u 87, a yayin da kasashe 58 suka nuna kin amuncewa da kudirin sai kuma 32 da sukayi rawar kuri'a.

Hakan dai ya sanya kudirin na Amurka bai samu rinjaye da yake bukata ba, ta yadda MDD, zatayi allawadai da kungiyar ta kungiyar ta Hamas.

A nasa bangare wakilin Isra'ila a MDD, nuna farincikinsa ya yi, wanda a cewarsa wannan shi ne karo na farko a tarihin MDD, da kasashe masu yawa ciki harda kungiyar tarayya Turai suka goyi bayan kudirin MDD na yi allawadai da kungiyar ta Hamas.

Saidai a nata bangare kungiyar ta Hamas, ta bakin kakakinta Sami Abou Zahri, watsi da yunkurin yin allawadai da kungiyar da MDD ta yi tamakar ''mari ne ga Amurka''. 

 

Tags