Dec 31, 2018 19:08 UTC
  • Kungiyar Hamas Ta Yaba Wa Iran Saboda Taimakon Da Take Yi Wa Palasdinawa

Wani kusa a kungiyar ta Hamas, Mushir al-Misry ya ce; Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana taimakawa alummar Palasdinu da kuma gwgawarmayarta kai tsaye

Al-Misry wanda shi ne shugaban kwamitin harkokin waje a Majalisar dokokin Palasdinu kuma kakakin wakilan Hamas a majlaisar, ya fadawa kamfanin dillancin labarun Nasim na Iran cewa; Gwagwarmayar al'ummar Palasdinu ta samar da sabon daidaito na karfi a tsakaninta da 'yan sahayoniya, tare da haramtawa 'yan sahayoniyar yin duk wani kutse a cikin yankin Gaza.

Al-Misry ya kara da cewa; matukar 'yan Sahayoniyar su ka yi tunanin kai wani farmaki akan yankin na Gaza, to za su dandana kudarsu.

Jami'in na kungiyar Hamas ya kuma kara da cewa; Ta hanyar aiki a tare tsakanin 'yan gwgawarmaya, sun iya samar da daidaito na karfi da 'yan sahayoniya, ta yadda idan su ka kai wa Gaza hari da makamai masu linzami to za a mayar musu da ruwan makamai masu linzami. Haka nan idan 'yan sahayoniyar su ka kashe wani Bapalasdine to za a halaka 'yan sahayoniya

Har ila yau, al-Misry ya yi watsi da yarjejeniyar karni wacce Amurka take son gabatarwa domin tilastawa Palasdinawa mika wuya ga 'yan sahayoniya, yana mai cewa ko kadan al'ummar Palasdinu ba za su bari hakan ta faru ba.

Tags