Pars Today
A wani bayani da jam'iyyun siyasar su ka fitar sun bukaci ganin an kafa majalisar rikon kwarya wacce za ta sami wakilcin jam'iyyun siyasar kasar domin fita daga halin da kasar take ciki
Rahotanni da suke fitowa daga birnin Khartum sun ce masu Zanga-zangar sun tasamma fadar shugaban kasar suna masu yin kira a gare shi da ya yi murabus
Shugaban kasar Sudan Umar Hassan Albashir ya yi alkawarin fitar da kasar daga matsalolin tattalin arzikin da ta fada ciki duk tare da cewa akwai yan tawaye a kasar
Shugaba Umar Hassan El Bashir na Sudan, ya bukaci 'yan sanda kasar dasu daina amfani da karfi fiye da kima kan masu zanga zanga tsadar rayuwa a kasar.
Shugaban jam'iyyar adawa ta Popular Congress, Umar al-Daqir ya kira yi dukkanin 'yan adawa da su hada kai domin kifar da gwamnatin Umar Hassan al-Bashir
Jam'iyyar "People Congress" ta kasar Sudan ta bukaci a gudanar da bincike kan kisan masu zanga-zanga da aka yi a makon da ya gabata.
Jakadan Kasar Kuwaiti a Sudan ne ya bayyana cewa kasarsa za ta taimaki Sudan domin ta fita daga matsalar tattalin arzikin da take ciki
A Sudan daruruwan mutane ne suka gudanar da zanga zanga a Khartoum babban birnin kasar yau Talata, a yayin da aka shiga kwana na bakwai a boran da ake kan tsadar rayuwa.
Jami'an tsaron sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu Zanga-zangar ta jiya da dare a babban birnin kasar Khartum
A wani bayani da sojojin kasar ta Sudan su ka fitar sun bayyana cikakken goyon bayansu ga gwamnatin shugaba Umar Hassan al-Bashir domin kare cigaban kasa