Sudan : Zanga zangar Tsadar Rayuwa Ta Yadu Zuwa Khartoum
A Sudan daruruwan mutane ne suka gudanar da zanga zanga a Khartoum babban birnin kasar yau Talata, a yayin da aka shiga kwana na bakwai a boran da ake kan tsadar rayuwa.
Saidai bayanai sun nuna cewa jami'an tsaro sun hana masu zanga zangar isa fadar shugaban kasar dake Khartoum.
A ranar 19 ga watan Disamba nan ne zanga zangar kan tsadar rayuwa ta barke a wasu sassan kasar ta Sudan, biyo bayan matakin gwamnati na kara kudin biredi a wannan kasa dake fama da tabarbarewar tattalin arziki.
Kusan dai wannan shi ne bore mafi muni da aka fuskanta a wannan kasa a kusa da shekaru talatin kan gwamnatin ta Umar el-Bashir dake shugabancin kasar tun 1989.
Wani rahoto da kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa, Amnesty International, ta fitar ya ce mutum 37 ne jami'an tsaro suka kashe tun farkon zanga zangar.
Rahoton da kungiyar ta fitar ya bukaci gwamnatin kasar data daina amfani da karfin tsaro waken murkushe masu zanga zangar.
Tuni dai wasu kasashen duniya da suka Biritaniya, Amurka, Norway da kuma Canada suka nuna damuwarsu akan lamarin tare da jadada 'yancin da al'ummar kasar ta Sudan keda shi na gudanar da zanga zangar lumana, tare da kira ga mahukuntan na Sudan dasu daina amfani da harsashen bindiga na gaske kan masu boren.