Kasar Kuwait Za Ta Taimak wa Kasar Sudan Da Kudade
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34575-kasar_kuwait_za_ta_taimak_wa_kasar_sudan_da_kudade
Jakadan Kasar Kuwaiti a Sudan ne ya bayyana cewa kasarsa za ta taimaki Sudan domin ta fita daga matsalar tattalin arzikin da take ciki
(last modified 2018-12-26T07:18:35+00:00 )
Dec 26, 2018 07:18 UTC
  • Kasar Kuwait Za Ta Taimak wa Kasar Sudan Da Kudade

Jakadan Kasar Kuwaiti a Sudan ne ya bayyana cewa kasarsa za ta taimaki Sudan domin ta fita daga matsalar tattalin arzikin da take ciki

Bassam Muhammad Mubarak al-Qabandi wanda ya gana da ministan harkokin wajen kasar ta Sudan al-Duraidy Muhammad Ahmad, ya jaddada matsayin kasarsa na taimakawa Sudan

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sudan ta kira yi jakadan na kasar Kuwaiti domin bayyana masa rashin jin dadinta akan kiran da ya yi wa mutanen Kuwaiti da su kaucewa ziyartar Sudan saboda halin da take ciki na Zanga-zanga.

Kusan mako guda kenan da al'ummar kasar Sudan suka fara gudanar da Zanga-zangar nuna kin yarda da daga farashin kayan masarufi da su ka hada da biredi da makamashi

Tun dai gwamnatin Sudan din ta kafa dokar ta baci a cikin wasu gundumomin kasar