Pars Today
Shugaban tawagar masu sa ido ta majalisar dinkin duniya a Sudan ta kudu ya nuna damuwarsa kan yadda rikici yake kara tsananin a dai-dai lokacinda ake kokarin fara taron sulhuntawa a tsakanin bangarorin da suke rikici a kasar.
Shugaban kasar Sudan ta Kudu Silva Kiir ya yi watsi da kiraye-kirayen yan adawar kasar na ya sauka daga kan kujerar shugabancin kasar idan yana son zaman lafiya ya dawo kasar.
Shugaba Salva Kiir, na Sudan ta Kudu, ya sallami ministan kudi na gwamnatinsa, Stephen Dhieu Dau, da kuma babban jami'in kula da horo da leken asiri na rundinar sojin kasar, Marial Chanoung.
Cikin wata wasika da ta aikewa kungiyar kasashen, Sudan ta kudu ta bukaci zama manba a cikin kungiyar.
Gwamnatin Sudan ta Kudu ta bayyana cewa duk wani matakin tsoma bakin kasashen yammacin Turai a harkokin cikin gidanta musamman daukan matakan matsin lamba kanta ba zasu taimaka wajen wanzar da zaman lafiya da sulhu a kasar ba.
Majalisar Dinkin Duniyar ce ta sanar da bullar fari a cikin sassa daban-daban na kasar Sudan Ta Kudun.
Hukumar Kolin Kula da 'Yan Gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi kan yiyuwar ci gaba da samun bullar matsalar 'yan gudun hijira a kasar Sudan ta Kudu.
Shugaban kasar Sudan ta kudu ya bayyana cewa gwamnatin Amirka ita ce sanadin tashin hankali da rikicin kasarsa
A jiya juma'a ne Majalisar Dinkin Duniyar ta fitar da rahoto da a ciki ta bayyana cewa yadda ake ci gaba da take hakkin bil'adama a kasar Sudan ta kudu
Wata kotu a Sudan ta Kudu ta yanke hukuncin kisa ga wani tsohon kanal na sojin Afrika ta Kudu, bisa tuhumarsa da yunkurin kifar da gwamnati.