Amirka Ita Ce Sanadin Rikicin Sudan Ta Kudu
Shugaban kasar Sudan ta kudu ya bayyana cewa gwamnatin Amirka ita ce sanadin tashin hankali da rikicin kasarsa
Cikin wani jawabi da ya gabatar a taron shugabanin kasashe manba a kungiyar bunkasa tattalin arzikin gabashin Afirka da ya gudana a birnin Kamfala na kasar Uganda, Shugaban kasar Sudan ta kudu Salva Kiir Mayardit ya bayyana gwamnatin Amirka a matsayin wacce ta samar da rikici a cikin kasarsa.
Shugaban kasar Sudan ta kudun ya ce matsin lambar da gwamnatin Amirke ke yi a kan gwamnatin Juba da kuma bayar da makamai ga 'yan tawayen na daga cikin abinda ya kawo tsaiko wajen dawo da konciyar hankali a kasar.
Har ila yau shugaba Salva Kiir Mayardit cikekken binciken da aka gudanar ya tabbatar da cewa gwamnatin Amirka ita ce ke taimakawa kungiyoyin 'yan tawayen dake yakar gwamnatin ta Juba.
Kasar Sudan ta Kudu dai ta fada cikin yakin basasa tun shekara ta 2013, shekaru biyu kacal bayan ballewarta daga kasar sudan. Kuma ya zuwa yanzu yaki tsakanin sojojin gwamnatin Shugaba Silvakir da kuma tsohun mataikinsa Reich Marchar ya lashe dubban rayukar mutanen kasar sannan ya tilastwa akalla miliyon guda tserewa daga gidajensu.