Sudan Ta Kudu Ta Bukaci Shiga Kungiyar Kasasen Larabawa
Cikin wata wasika da ta aikewa kungiyar kasashen, Sudan ta kudu ta bukaci zama manba a cikin kungiyar.
Wannan bukata ta sudan ta kudu za a tattauna ta a zaman ministocin kasashen wajen larabawa karo na 149 da zai gudanar a wannan laraba.
Bayan da kasar sudan ta kudu ta balle daga Sudan, kungiyar kasashen Larabawan ta gindaya mata sharadin na cewa matukar tana son kasancewa manba a cikin kungiyar to ya zama wajibi ta zabi yaran larabci a matsayin yaran da hukuma take amfani da shi a cikin kasar, a halin yanzu dai kasar ta amfani da yaran turanci na Inglishi.
A halin da ake cikin kasar sudan ta kudun nada kyakkyawar alaka da wasu kasashen Larabawa, ciki kuwa harda kasar Masar, a bangare guda hukumomin birnin Khartoum na dora alhakin balewar sudan ta kudun daga kasar ga haramtacciyar kasar Isra'ila.
A ranar 9 ga watan yunin 2011 ne sudan ta kudu ta samu 'yancin kai daga kasar Sudan.