Sudan Ta Kudu Ta Maida Martani Kan Tsoma Bakin Kasashen Turai A Harkokin Kasarta
Gwamnatin Sudan ta Kudu ta bayyana cewa duk wani matakin tsoma bakin kasashen yammacin Turai a harkokin cikin gidanta musamman daukan matakan matsin lamba kanta ba zasu taimaka wajen wanzar da zaman lafiya da sulhu a kasar ba.
A taron manema labarai da ya gudanar a birnin Juba fadar mulkin kasar Sudan ta Kudu: Ministan watsa labaran kasar Michael Makuei ya bayyana cewa: Gwamnatin Sudan ta Kudu tana shirye ta koma kan kujerar tattaunawa da bangaren 'yan tawayen kasar a birnin Adis Ababa na kasar Habasha da nufin rayar da shirin neman wanzar da zaman lafiya da sulhu a kasar Sudan ta Kudu.
Makuei ya kara da cewa: Sudan ta Kudu ba zata taba lamintar matsin lamba da barazana daga bangaren kasashen yammacin Turai ba musamman kasashen Amurka da Birtaniya da suka sanyo ta gaba.