Pars Today
Rahotanni daga Jamus na cewa ana gudanar da bincike a gidajen iyalan wasu mutane biyu da ake zargi da taimakawa kungiyoyi jihadi na Syria.
Iran ta sanar da cewa wasu daga cikin kamfanonin manyan kasashen turai za su shiga yin aiki tare da Iran a bangaren makamashi na Petrochemical.
An gudanar da janazar musulmin da suka yi shahada a lokacin da wani dan ta'adda ya bude wutar bindiga a kansu a lokacin da suke salla a cikin masallacin birnin Quebec na kasar Canada
An rufe wasu manyan masallatai guda hudu na musulmi a wasu manyan biranan kasar Holland biyo bayan harin da aka kai kan wani masallaci a kasar Canada tare da kashe masallata.
Shugabannin kasashe bakwai na kudancin kungiyar tarayya Turai ta EU na soma wani taro yau a birnin Lisbonne da nufin samar da mafita dangane da kalubalen dake gaban kasashen.
Wasu alkalumma na gwamnatin kasar Italiya sun yi nuni da cewa, addinin muslunci shi ne addini na biyu da ke yaduwa a cikin kasar, domin kuwa fiye da kashi 34 cikin dari na 'yan kasashen waje da ke zaune a kasar musulmi ne.
Wajibi ga dukkanin musulmi su shiga cikin fagen dagar yakin da masu girman kai su ke yi da musulmi.
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar rashin kula da kuma girmama koyarwa ta addini da umurnin Ubangiji, su ne ummul aba'isin din matsalolin da kasashen Yammacin suke fuskanta duk kuwa da irin ci gaban ilimi da suke da su.
Magatakardan majalisar shawara ta tarayyar Turai ya jaddada wajibcin ci gaba da tattaunawa da kasar kan sabanin da ta suka shiga tsakanin bangarorin biyu a shekaru baya bayan nan.
Jami'an kwana-kwana na kungiyar tarayyar Turai da suke sanya ido kan fataucin bakin haure a tekun Mediterranea sun samu nasarar tseratar da bakin haure fiye da 200 daga halaka.