An Rufe Manyan Masallatan Kasar Holland Guda Hudu
An rufe wasu manyan masallatai guda hudu na musulmi a wasu manyan biranan kasar Holland biyo bayan harin da aka kai kan wani masallaci a kasar Canada tare da kashe masallata.
Kamfanin dillancin labaran IQNA ya nakalto daga shafin arabi ya bayar da rahoton cewa, wadannan masallatai guda hudu da aka rufe suna biranan Amstardam, Watardam da kuma Hague ne, kuma an rufe masallatan ne bisa bukatar manyan cibiyoyin musulmi na kasar.
A cikin wani bayani na hadin gwaiwa da cibiyoyin musulmin kasar Holand da suke kula da masallatai suka fitar, sun bayyana cewa akwai barazanar tsaro a yankunan da wadannan masallatai suke, kuma abin da ya faru a kasar Canada na kisan musulmi 6 da suke salla a cikin masallaci, ya sanya dole ne a dakatar da ayyuka a wadannan masallatai zuwa wani lokaci nan gaba.
Kasar Holland na daga cikin kasashen da aka fara samun kungiyoyin da suka fara bayyana kiyayya ga musulmia cikin kasashen yammacin turai, lamarin da ya samu wurin zama hatta a tsakanin 'yan siyasa.
Harin da wasu masu tsananin kyamar musulmi suka kai a kan wani masallaci a kasar Canada dai ya yi sanadiyyar shahadar masallata 6 tare da jikkatar wasu.