Ana Bincike Gidajen Iyalan Mayakan Jihadi A Jamus
Feb 08, 2017 11:17 UTC
Rahotanni daga Jamus na cewa ana gudanar da bincike a gidajen iyalan wasu mutane biyu da ake zargi da taimakawa kungiyoyi jihadi na Syria.
Ana dai zargin mutanen biyu ne da taimakawa tsohuwar kungiyar Al'Nosra reshen Al-Qaida a Syria da kayan agaji, kamar yadda offishin mai shiga da kara kan ayyukan ta'addanci na Jamus ya sanar.
Mutanen biyu da ba'a bayyana sunayensu ana kuma zarginsu da taimakawa kungiyar da dau sunan Fateh al-Cham a yanzu bayan raba gari da Al-Qaida, da motocin daukar marasa lafiya da na'urorin binciken lafiya da magunguna da kuma kayan abunci.
Wadanda ake zargin dai sunyi mu'amula da kungiyoyin agaji na Jamus ciki harda kungiyar likitoci marar iyaka ta MSF.
Tags