Pars Today
Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Shamkhani ya bayyana cewar kasashen Iran, Rasha da Turkiyya ba su aike wa Amurka da wata gayyyata ta hadin gwiwa da nufin ta halarcin taron sulhunta rikicin kasar Siriya da za a gudanar a kasar Kazakhstan ba yana mai cewa ko da Amurkan ta zo to babu wata rawa da za ta taka a tattaunawar.
Rahotanni daga Turkiyya na cewa an binne dan sanda nan daya hareb har lahira jakadan kasar Rasha a birnin Ankara a wani wuri da ba'a bayyana ba.
Bayanai da kafofin yadda labarai daga Turkiyya ke rawaitowa na cewa, maharin nan daya kashe mutane da dama a wani gidan rawa a safiyar 1 ga watan nan, mayakin jihadi ne na kungiyar IS dan asalin kasar Uzbekistan.
Hukumomi a kasar Turkiyya na ci gaba da farautar mutumin nan daya kashe mutane 39 a wani gidan rawa dake birnin Istambul.
Majalisar Dokokin kasar Turkiyya ta amince da kara wa'adin dokar ta bacin da aka sanya a kasar tun bayan juyin mulkin sojin da bai yi nasara a kasar ba a watan Yulin da ya gabata, zuwa watanni uku masu zuwa.
Rahotanni daga Turkiyya na cewa mutane 16 ne kawo yanzu aka cafke bisa zarginsu da hannu a harin da wani dan bindiga ya kai a gidan rawan na Reina dake birnin Istambul.
A kalla mutane 39 ne suka hallaka a yayin da wani dan bindiga da yayi shigar burtu ya bude wuta a wani gidan rawa dake birnin Istanbul na kasar Turkiyya.
Firayi ministan kasar Iraki Haider al-Abadi ya kirayi shugaban kasar Turkiyya Rajab Tayyib Erdogan da ya girmama hurumin kasar Irakin da kuma kokari wajen kyautata alaka ta makwabtaka da 'yan'uwantaka tsakanin kasashen biyun.
Gwamnatin kasar Turkia ta bukaci tsagaita bude wuta tsakanin sojojin kasar Siria ta kawayensu da kuma yan ta'adda a duk fadin kasar.
Jakadan Turkiya A Iraki ya ce sojojin kasarsa za su fice daga cikin kasar Iraki