Turkiyya : Ana Ci gaba da Farutar Maharin Daya Kashe Mutane 39
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i16132-turkiyya_ana_ci_gaba_da_farutar_maharin_daya_kashe_mutane_39
Hukumomi a kasar Turkiyya na ci gaba da farautar mutumin nan daya kashe mutane 39 a wani gidan rawa dake birnin Istambul.
(last modified 2018-08-22T11:29:29+00:00 )
Jan 05, 2017 11:57 UTC
  • Turkiyya : Ana Ci gaba da Farutar Maharin Daya Kashe Mutane 39

Hukumomi a kasar Turkiyya na ci gaba da farautar mutumin nan daya kashe mutane 39 a wani gidan rawa dake birnin Istambul.

Kawo yanzu dai mutane akalla 36 ne aka cafke bisa zarginsu da hannu a harin da aka kai da sanyin safiyar ranar 1 ga watan nan.

ko a wannan safiyar ma an ce an cafke mutane da dama a yankin Silivri dake kusa birnin na Istambul a cawar kanfanin dilancin labaren kasar na kusa da gwamnati Anadolu.

A halin da ake ciki dai hukumomin kasar sun wallafa hotinan mutimun wanda har yanzu dai ana tababa aka asalinsa, yayin da kungiyar 'yan ta'addan IS ta dauki alhakin kai harin.