Turkiyya : An Binne Mutumin Daya Harbe Jakadan Rasha A Boyayen Wuri
Rahotanni daga Turkiyya na cewa an binne dan sanda nan daya hareb har lahira jakadan kasar Rasha a birnin Ankara a wani wuri da ba'a bayyana ba.
kamar yadda kanfanin dilancin labaren Anadolu ya rawaito ya ce, bayan shafe wa'adin da aka bayar babu wanda ya zo neman gawar dan sanda, an mika gawarsa ga da'irar birnin wace ta binne shi a wani wuri da ba'a bayyana ba.
A ranar 19 ga wtan Disamba daya gabata ne dan sanda mai suna Mevlüt Mert Altintas, dan shekaru 22 a duniya ya harbe har lahira Andreï Karlov jakadan kasar Rasha a Turkiyya a lokacin da yake jawabi a wani taro a birnin Ankara.
Dan Sanda wanda shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana a matsayin mai biyaya ga shehun malamin nan dan kasar dake gudun hijira a Amurka wato Fethullah Gülen, yayi ta kiran Allahu Akbar Akbar kafin ya bude wuta kan jakadan na Rasha, kuma a lokacin ne shi ma jami'an tsaro dake wurin suka hallaka shi.