Turkiyya : Maharin Daya Kashe Mutane 39 Dan Uzbekistan Ne
Bayanai da kafofin yadda labarai daga Turkiyya ke rawaitowa na cewa, maharin nan daya kashe mutane da dama a wani gidan rawa a safiyar 1 ga watan nan, mayakin jihadi ne na kungiyar IS dan asalin kasar Uzbekistan.
Maharin wanda ake cikin farautarsa har kawo yanzu ya kashe mutane 39 galibi 'yan kasashen waje a gidan rawa Raina dake birnin Istambul a lokacin da ake bukukuwan shiga sabuwa shekara.
Tun da farko dai an bayyana maharin wanda aka wallafa hotunansa da cewa dan asalin Kirghizstan ne.
Amman yanzu jami'an leken asiri da 'yan sanda yaki da ta'addanci na kasar ta Turkioyya sun bayyana mutumin dan shakaru 34 da cewa dan asalin kasar Uzbekistan ne dake cikin kungiyar 'yan ta'addan IS reshen Asiya, wanda wasu kafofin yada labaren suka ce sunansa na yaki shi ne Abou Mohammad Khorassani, saidai babu wata kafa ko majiyar gwamnati data tabbatar da hakan.