Pars Today
Gwamnatin kasar Turkiya ta bada sanarwan cewa tun bayan juyin mulkin da bai sami nasara a kasar a shekara ta 2016 ya zuwa yanzun kotuna daban-daban a kasar sun yanke hukuncin zaman kaso na tsawon rayuwa kan mutane a kimani 2000.
Rahotanni daga Turkiyya na cewa mutane tara ne suka rasa rayukansu, kana wasu hamsin na daban suka raunana a wani hatsarin tsakanin wani jirgin kasa mai gundun-tsiya da wani karamin jirgin kasa na daban.
Kasar Turkiyya ta bayyana cewar tana tattaunawa da Majalisar Dinkin Duniya dangane da batun gudanar da bincike kan kisan gillan da aka yi wa dan jaridar nan dan kasar Saudiyya, Jamal Khashoggi a karamin ofishin jakadancin Saudiyyan da ke birnin Istanbul na kasar Turkiyyan.
'Yan sandan kasar Turkiyya sun kai wani samame wani katafaren gida da ke arewa maso gabashin lardin Yalova na kasar a ci gaba da binciken da suke gudanar kan kisan gillan da aka yi wa dan jaridar kasar Saudiyya din nan mai suka gwamnatin kasar Jamal Khashoggi a karamin ofishin jakadancin Saudiyyan da ke birnin Istanbul.
Gwamnatin Turkiyya ta sanar da mutuwar sojinta hudu a wani hatsarin jirgin soji mai saukar ungulu a tsakiyar birnin Santambul.
Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyyya, ya bayyana cewa sun bai wa kasashen Saudiyya, Amurka, da Jamus da Faransa da kuma Ingila hoton bidiyon kisan dan jaridan Jamel Kashoggi.
Saudiyya ta yi watsi da bukatar Turkiyya na a mika mata wasu 'yan Saudiyyar su 18 da ake zargi da kashe dan jaridan nan Jamel Khashoggi a karamin ofishin jakadancin Saudiyyar na Santanbul.
Shugabannin kasashen Rasha, Faransa, Turkiyya da kuma Jamus na wani taro a birnin Santanbul kan batun Siriya.
Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Rouhani yayi Allah wadai da kisan gillan da aka yi wa Jamal Khashoggi, sanannen dan jaridar kasar Saudiyyan nan yana mai bayyana cewar kisan gillan da aka yi masa wata babbar jarabawa ce ga masu ikirarin kare hakkokin bil'adama.
Cikin wani jawabi da ya gabatar gaban magoya bayansa a wannan talata, Shugaba Erdugan ya yi karin haske kan yadda aka hallaka Jamal Khashoggi a karamin offishin jakasancin Saudiya dake birnin Istambul