Khashoggi : Saudiyya Ta Ce Ba Zata Mika Wadanda Ake Zargi Ba
Saudiyya ta yi watsi da bukatar Turkiyya na a mika mata wasu 'yan Saudiyyar su 18 da ake zargi da kashe dan jaridan nan Jamel Khashoggi a karamin ofishin jakadancin Saudiyyar na Santanbul.
Da yake sanar da hakan a wani taro kan sha'anin tsaro a birnin Manama, ministan harkokin wajen kasar ta Saudiyya Adel al-Jubeir, ya ce mutanen da ake zargi 'yan Saudiyya ne, kuma ana tsare dasu a Saudiyya, sannan a Saudiyya ake binkice kansu, a don haka babu batun mika mutanen ga Turkiyya, inji shi.
Mahukuntan Ankara dai sun bukaci Saudiyya data mika masu mutanen guda 18 don tayi musu shari'a saboda a karamin ofishin jakadancin Santanbul aka kashe dan jaridan Khashoggi.
Turkiyya dai ta nace kan cewa jami'an da suka fito daga Riyad sun jima suna shirya yadda za'a kashe dan jaridan.
Bayan fusknatar matsin lamba daga kasashen duniya, a ranar Asabar data gabata ne Saudiyya ta amince cewa an kashe dan jaridan a karamin ofishin jakadancin na ta, bayan shafe dogon lokaci tana musanta hakan.