Turkiyya Ta Bai Wa Wasu Kasashe Bidiyon Kisan Khashoggi
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i34030-turkiyya_ta_bai_wa_wasu_kasashe_bidiyon_kisan_khashoggi
Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyyya, ya bayyana cewa sun bai wa kasashen Saudiyya, Amurka, da Jamus da Faransa da kuma Ingila hoton bidiyon kisan dan jaridan Jamel Kashoggi.
(last modified 2018-11-11T06:13:51+00:00 )
Nov 11, 2018 05:40 UTC
  • Turkiyya Ta Bai Wa Wasu Kasashe Bidiyon Kisan Khashoggi

Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyyya, ya bayyana cewa sun bai wa kasashen Saudiyya, Amurka, da Jamus da Faransa da kuma Ingila hoton bidiyon kisan dan jaridan Jamel Kashoggi.

Fadar shugaban kasar ta kuma ce an saurari sautukan kan abunda ya faru ga dan jaridan, saidai babu wani bayyani a rubuce da aka yada. 

Erdogan ya kuma nanata cewa Saudiyya ta san wanda ya kashe dan Jaridan.

A ranar 2 ga watan Oktoba da ya gabata ne aka kashe dan jaridan mai sharhi dake sukan manufofin masarautar Saudiyya, Jamal Kashoggi a cikin karamin ofishin jakadancin Saudiyya dake birnin Santanbul na kasar Turkiyya, har yanzu kuma ba a ga gawarsa ba, wacce Turkiyya ta ce an narka ta ne cikin sinadarin asid.

Saudiyya dai ta musanta hannu duk wani dan gidan Sarautar kasar a kisan dan jaridan.