Turkey Ta Ce Tana Tattaunawa Da MDD Kan Binciken Kashe Khashoggi
(last modified Tue, 11 Dec 2018 16:23:53 GMT )
Dec 11, 2018 16:23 UTC
  • Turkey Ta Ce Tana Tattaunawa Da MDD Kan Binciken Kashe Khashoggi

Kasar Turkiyya ta bayyana cewar tana tattaunawa da Majalisar Dinkin Duniya dangane da batun gudanar da bincike kan kisan gillan da aka yi wa dan jaridar nan dan kasar Saudiyya, Jamal Khashoggi a karamin ofishin jakadancin Saudiyyan da ke birnin Istanbul na kasar Turkiyyan.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar ministan harkokin wajen kasar  Turkiyyan Mevlut Cavusoglu ne ya sanar da hakan a yau Talata inda yace suna ci gaba da tattaunawa da MDD kan gudanar da bincike na  kasa da kasa  kan kisan gillan da aka yi wa Khashoggin biyo bayan ci gaba da bukatar hakan da ake ta gabatar wa gwamnatin ta Turkiyya.

Ministan harkokin wajen na Turkiyyan ya ce a baya dai fatan da suke da shi shi ne cewa kada lamarin ya kai ga binciken kasa da kasa din da a ce Saudiyya din ta ba da hadin kan da ake bukata wajen gano wadanda suke da hannu cikin kisan gillan.

A makon da ya wuce ne shugabar hukumar kare hakkokin bil'adama ta MDD, Michelle Bachelet ta sanar da cewa akwai bukatar gudanar da bincike na kasa da kasa don gano wadanda suke da hannu cikin kisan gillan da aka yi wa Khashoggi a a karamin ofishin jakadancin Saudiyyan da ke birnin Istanbul na kasar Turkiyyan a ranar 2 ga watan Oktoban da ya gabata.