Pars Today
Majalisar tarayyar turai ta bukaci ganin kasashen Saudiyya da Hadaddiyar Daular larabawa da su kaucewa hargitsa zaman lafiya a kasar Somaliya
Rahotani dake fitowa daga gwamnatin Faransa na nuni da cewa a farko watani shida na wannan shekara, Paris ta sayar da makamai na dala bilyan uku da miliyan 920 ga wasu kasashen Larabawa na yankin gabas ta tsakiya.
Kungiyar tarayyar Afrika ta yi Allah wadai da shishigin da wasu kasashen waje suke yi a kasar Somalia, ta kuma kara da cewa hakan zai iya gurgunta kokarin dawo da zaman lafiaya a kasar.
Shugaban kungiyar Tarayyar Afrika ya bayyana damuwarsa kan yadda wasu kasashen waje musamman da ba na Afrika ba suke tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Somaliya.
Gwamnatin kasar Kenya ta gargadi wasu daga cikin kasashen larabawan yankin tekun Fasha musamman UAE dangane da ci gaba da dagula lamurra da suke yi a kasar Somalia.
Sakamakon rashin jituwar da ya kunno kai tsakanin hadaddiyar daular larabawa (UAE) da kuma gwamnatin Somalia, a jiya UAE ta rufe babban asibitin Sheikh Zayid da ke Magadishu.
Kasar Somaliya ta dakatar da kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) daga shirin da take aiwatarwa a kasar na ba da horo ga daruruwan sojojin kasar a wata alama da ke nuni da irin tsamin da alakar da ke tsakanin kasashen biyu ta ke ci gaba da yi.
Muftin kasar Libiya yayi kakkausar suka ga abin da ya kira irin makudan kudaden da Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa suke kashewa wajen biyan bukatun Sahyoniyawa da kuma haifar da rashin tsaro da fitina a yankin Gabas ta tsakiya da kuma Arewacin Afirka.
Majalisar Dokokin Kasar Somaliya ta kada kuri'ar rashin amincewa da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin bangarori uku wato kasar Habasha da Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Somaliland da ke cin kwarya-kwaryar gashin kai a kasar Somaliya.
'Yan awaren da suka dauki kwanaki uku suna fada da sojojin gwamnatin Hadi Mansur mai murabus, sun kwace da birnin Aden a yau talata.