Alaka Na Ci Gaba Da Kara Yin Tsami Tsakanin Somalia Da UAE
(last modified Wed, 18 Apr 2018 06:41:07 GMT )
Apr 18, 2018 06:41 UTC
  • Alaka Na Ci Gaba Da Kara Yin Tsami Tsakanin Somalia Da UAE

Sakamakon rashin jituwar da ya kunno kai tsakanin hadaddiyar daular larabawa (UAE) da kuma gwamnatin Somalia, a jiya UAE ta rufe babban asibitin Sheikh Zayid da ke Magadishu.

Rahotanni sun ce hadaddiyar daular larabawa ta sanar da cewa ta rufe babban asibin nata da ke birnin Magadishou har sai abin da hali ya yi, tare da kwashe kayayyakin aiki da ke asibitin da kuma kiran ma'aikatan asibitin da su dawo gida.

Wannan mataki dai ya zo ne biyo bayan kwace wasu makudan kudade UAE  har dala miliyan 10 da jami'an tsaron Somalia suka yi ne a filin sauka da tashin jiragen sama na Magadishou da ake nufin fita da su daga kasar.

Dangantaka ta yi tsami ne tsakanin UAE da Somalia, tun bayan da gwamnatin Somalia ta nuna goyon bayanta ga kasar Qatar,a  rikicin da ake yi tsakaninta da kasashen Saudiyya, UAE, Bahrain da kuma Masar.