Yan Awaren Kudancin Yemen Sun Kwace Iko Da Birnin Aden
Jan 30, 2018 18:57 UTC
'Yan awaren da suka dauki kwanaki uku suna fada da sojojin gwamnatin Hadi Mansur mai murabus, sun kwace da birnin Aden a yau talata.
Tun da fari rahotanni da suke fitowa daga birnin na Aden sun ce 'yan awaren sun killace fadar gwamnati a Aden, inda piraminista da wasu ministocin gwamnatin mai murabus, suke ciki.
Bugu da kari, sansanin sojan motoci masu silke da ke tsaron fadar gwamnati ya shiga karkashin ikon 'yan aware, wanda ya zama babban koma baya ga gwamnatin Abdulhadi Mansur wadda Saudiyya take goyon baya.
Ana kallon sabon rikicin da ya barke a matsayin nuna kwanji a tsakanin Hadaddiyar Daular Larabawa da Saudiyya.
Tags