Tarayyar Turai Ta Sake Gargadi Akan Tsoma Bakin Saudiyya A Kasar Somaliya
Majalisar tarayyar turai ta bukaci ganin kasashen Saudiyya da Hadaddiyar Daular larabawa da su kaucewa hargitsa zaman lafiya a kasar Somaliya
Bayanin da majalisar tarayyar turai din ta fitar ya kuma ci gaba da cewa; Yanke taimakon kudaden da Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa su ka yi ga gwamnatin kasar ta Somaliya ya raunana jami'an tsaron kasar.
Watanni biyu da su ka gabata ma dai jakadun kasashen tarayyar turai a gabacin nahiyar Afirka sun yi taro a kasar Uganda inda su ka yi gargadi akan tadda kasashen larabawan yankin tekun pasha suke tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Somaliya.
Bugu da kari ana zargin kasashen da taimakawa wasu bangarori na kasar da hakan yake jawo sabani na siyasa a cikin kasar.