Pars Today
Gwamnatin Venezuela ta yi kakkausar suka da kuma Allah wadai da tsoma bakin da Amurka ta yi cikin harkokin zaben da aka gudanar a kasar tana mai bayyana hakan a matsayin gazawar Amurka wajen cimma bakar aniyar da take da ita kan kasar Venezuelan.
Shugaban kasar Venezuala ya jaddada cewa: Al'ummar Venezuala suna cikin shirin kalubalantar duk wani makircin kasar Amurka musamman matakin wuce gona da iri kan kasarsu.
Shugaba Nicolas Mdduro na kasar Venezuela, zai tsaya takara a zaben shugabancin kasar na shekara 2018 dake tafe, kamar yadda mataimakin shugaban kasar Tareck El Aissami ya sanar a yau Laraba.
Ma'aikatar Kudi na kasar Amurka ta bada labarin cewa gwamnatin kasar zata bayyana wani shiri na kara dorawa wasu karin manya-manyan jami'an gwamnatin kasar Venezuela takunkumai.
Wakilin kasar ta Venezuela a Majalisar Dinkin Duniyar Rafael Ramírez ya bukaci MDD da ta kaucewa aiki da manufofin Amurka.
Ministan harkokin wajen kasar Venezuela Jorge Arasasa ya nuna rashin amincewarsa ga jawaban shugaban kasar Amurka da kuma Priministan kasar Espania a jiya Talata, ya kuma kara da cewa jawaban nasu shishigi ne a cikin lamurran cikin gida na kasar.
Ministan aikin gona a kasar Venezuala ya bayyana cewa: Shugaban kasar Amurka ne ke juya akalar wasu shugabannin kasashen latin Amurka.
Shugaba Nicolas Maduro na Venezuella, ya tabbatar a Jiya Juma'a cewa, an kusa cimma yarjejeniya da 'yan adawa kan kawo karshen rikicin siyasar kasar.
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada goyon bayansa ga shirin gudanar da zaman tattaunawa tsakanin gwamnatin Venezuala da 'yan adawar kasar da nufin neman hanyar warware rikicin siyasar kasar ta hanyar lumana.
MDD ta bayyana matukar damuwa akan abunda ta kira tsaka mai wuya da tsarin demokuraddiya yake ciki a kasar Venezuella.