MDD : Demokradiyya Na Cikin Tsaka Mai Wuya A Venezuela
(last modified Wed, 30 Aug 2017 16:26:49 GMT )
Aug 30, 2017 16:26 UTC
  • MDD : Demokradiyya Na Cikin Tsaka Mai Wuya A Venezuela

MDD ta bayyana matukar damuwa akan abunda ta kira tsaka mai wuya da tsarin demokuraddiya yake ciki a kasar Venezuella.

A rahoton data fitar yau a Geneva, MDD ta yi gargadin cewa karuwar take hakkokin bil’adama a Venezuela na kawo cikas ga Demokradiyyar kasar.

Rahoton wanda hukumar kare hakkin bil adama ta MDD ta fiyar ya nuna matukar damuwa akan yadda ake muzgudanawa 'yan adawa da kuma sanya fargaba a cikin rayuwa al'ummar kasar domin kawo karshen zanga-zanga.

Babban kwamishinan hukumar, Zeid Ra'ad Al Hussein, ya yi gargadin cewa tabarbarewar tattalin arziki da rikicin siyasa da ake fama da shi zai iya iya jefa kasar ta Venezuella cikin mawuyacin  hali.

Wannan rahoton na zuwa ne kwana guda bayan kallamen da shugaban kasar Faransa, Emanuelle Macron ya yi na danganta mulkin shugaban Venezuela da na kama karya, batun da gwamnatin Karakas ta danganta da shishigi a harkokin cikin gidan kasar.