Venezuela : Maduro Zai Yi Takara A 2018
Shugaba Nicolas Mdduro na kasar Venezuela, zai tsaya takara a zaben shugabancin kasar na shekara 2018 dake tafe, kamar yadda mataimakin shugaban kasar Tareck El Aissami ya sanar a yau Laraba.
Mista El Aissami ya fada a wani taron jam'iyyar 'yan gurguzu mai mulki a kasar (PSUV) cewa da yardar Allah da al'ummar kasar zasu sake zaben dan uwansu Maduro a shekara 2018 mai zuwa.
A watan Disamba mai zuwa ne aka sa ran gudanar da babban zaben kasar mai arzikin man fetur, koda yake wasu masu sharhi na cewa gwamnatin kasar zata iya gusa zaben zuwa watan Maris na shekara mai zuwa.
A halin da ake ciki dai kasar Venezuwela na fuskantar dimbin bashi da rikicin siyasa wanda kawo yanzu ya yi sanadin mutuwar mutane 125.
Gwamnatin ksar dai ta shirya hawa teburin tattaunawa da jam'iyyar 'yan adawa ta MUD domin kawo karshen rikicin siyasar dake zaman karfen kafa ga ci gaban kasar.