Jan 08, 2017 06:37
Rahotanni daga kasar Ivory Coast sun bayyana cewar a safiyar Lahadi sojoji masu bore a kasar sun sako ministan tsaron kasar Alain-Richard Donwahi bayan garkuwa da suka yi da shi na sa'oi a wani gida da ke birnin Bouake inda sojojin suka fara yin boren.