Wani Ministan A Gwamnatin Sudan Ta Kudu Ya Hadewa Yan Tawaye
(last modified Sat, 18 Feb 2017 11:56:35 GMT )
Feb 18, 2017 11:56 UTC
  • Wani Ministan A Gwamnatin Sudan Ta Kudu Ya Hadewa Yan Tawaye

Ministan ayyuka na gwamnatin Sudan ta Kudu ya bada sanrwan ajiye aikinsa da kuma hadewarsa da yan tawaye karkashin Rieck Masher.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayyana cewa General Joobiril Dooblom ya bada wannan sanarwan ne a cikin wata wasika mai shafi guda wanda ya bari a ofishinsa a makon da ya gabata.

Dobblom dai shi ne jami'an gwamnatin Sudan na Kudu na biyu da ya ajiye aikinsa a makon da ya gabata.

Kafin sa   Thomas Cirillo Swaka  jami'i a bangaren tallafin gaggawa na sojojin kasar ya ajiye aikinsa , sai dai shi bai bayyana cewa ya hadewa kungiyar yan tawaye ba. Sannan kafin ya ajiye aiki gwamnatin kasar ta bada sanarwan cewa yana daga cikin wadanda ake za'a yi masu bincike kan yin sama da fadi da kudaden jama'a.