Sabbin Rahotanni Kan Kisan Fararen Hula A Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya
Feb 18, 2017 07:53 UTC
Kungiyoyin kare hakkin bil adama da ke sanya ido a jamhuriyar Afirka ta tsakiya, sun fitar da wani rahoto kan kisan fararen hula a wasu yankuna na kasar.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya bayar da rahoton cewa, kungiyar UPC ce ke da alhakin kisan fararen hula 32 a Bakala da ke tsakiyar kasar, bayanin ya ce an kisan ne tun a cikin watan Disamban da ya gabata, amma ba iya gano wadanda ke da hannu cikin lamarin ba.
Rahoton ya ce bayan gudanar da binciken kwakwaf kan abin da ya faru, an gano cewa kungiyar ta UPC ce ta aikata hakan, tare da yin kira ga mahukuntan kasar da kuma na majalisar dinkin duniya, da a dauki matakan shari'a a kan wannan lamari.
Tags