"Yan tawayen Kasar Uganda Sun Kai Hari A Gabacin Kasar Congo
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i15994-yan_tawayen_kasar_uganda_sun_kai_hari_a_gabacin_kasar_congo
Yan tawayen kasar Uganda da aka fi sani da (ADF) sun kai hari a yankunan (Samboko) da ( Bialee) da su ke kan iyaka,inda su ka kashe mutane 14.
(last modified 2018-08-22T11:29:28+00:00 )
Jan 02, 2017 11:46 UTC

Yan tawayen kasar Uganda da aka fi sani da (ADF) sun kai hari a yankunan (Samboko) da ( Bialee) da su ke kan iyaka,inda su ka kashe mutane 14.

Radiyo Okapi na kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ya ambaci cewa; Yan tawayen kasar Uganda da aka fi sani da (ADF) sun kai hari a yankunan (Samboko) da ( Bialee) da su ke kan iyaka,inda su ka kashe mutane 14.

Radiyon ya kuma ambato jami'n tafiyar da mulki a gundumar Kivo ta arewa, Gilli Gotabo, yana yin kira da a dauki matakai na tsaro ta hanyar aikewa da sojoji da kuma 'yan sanda.

Bugu da kari jami'in ya ce; Ana yawan samun kashe mutane a cikin yankin.

'Yan tawayen kasar ta Uganda dai suna yawan kai wa fararen hula da su ke a gabacin kasar ta Jamhuriyar demokradiyyar Congo hare-hare.