-
Martanin Kungiyar Ansarullah Ta Kasar Yemen Kan Da'awar Saudiya
Oct 29, 2016 02:19Kakakin kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya ce da'awar da Saudi-Arabiya ta yi na cewa kungiyar ta kai hari kan garin Makka, yunkuri ne na sanya rudani a tsakanin Al'ummar musulmi.
-
Sojojin Yamen Sun Kashe Sojojin Mamayar Saudiyya Da Dama A Arewa Maso Yammacin Kasar
Oct 21, 2016 01:24A wani sabon gumurzu da aka yi tsakanin sojojin kasar Yamen da sojojin mamayar masarautar Saudiyya a yankunan da suke arewa maso yammacin kasar ta Yamen; sojin Saudiyya da dama ne suka halaka, yayin da wasu adadi na daban suka jikkata.
-
An Fara Aiki Da Shirin Dakatar Da Bude Wuta A Yemen
Oct 20, 2016 02:16Dukkanin bangarori sun fara aiki da shirin dakatar da bude wuta na kwanaki uku a kasar Yemen daga yau Alhamis, wanda za a iya kara tsawon wa'adinsa a lokuta masu zuwa.
-
An Sanar Da Shirin Tsagaita Wuta A Yemen
Oct 18, 2016 14:47MDD, ta sanar da shirin tsagaita buda wuta na Sa’o’I 72 a kasar Yemen, wace za ta soma aiki daga ranar Alhamis mai zuwa.
-
Kungiyar Ansarullah Ta Bukaci Gudanar Da Binciken Kasa Da Kasa Kan Harin Saudiyya Wajen Jana'iza A Yemen
Oct 17, 2016 02:23Kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen da aka fi sani da kungiyar 'yan Houthi ta bukaci da a gudanar da binciken kasa da kasa dangane da harin wuce gona da irin da Saudiyya ta kai wajen jana'iza a birnin Sana'a da yayi sanadiyyar mutuwar alal akalla mutane 140.
-
Za A Fitar Da Wadanda Saudiyya Ta Jikka A Yemen Zuwa Asibitocin Kasashen Ketare
Oct 15, 2016 13:27Wasu daga cikin wadanda suka samu munanan raunuka a harin da jiragen yakin Saudiyya suka kaddamar kan fararen hula a birnin Sana'a na Yemen za su samu kulawa a wasu asibitoci na kasashen ketare.
-
Jiragen Saman Yakin Saudiyya Suna Ci Gaba Da Kai Hare Hare Kan Kasar Yamen
Oct 15, 2016 02:49Jiragen saman yakin masarautar Saudiyya sun kai hare-haren wuce gona da iri kan yankunan kasar Yamen lamarin da yi sanadiyyar mutuwar fararen hula ciki har da kananan yara.
-
Gwamnatin Kasar Britania Zata Gabatar Da Wani Shiri Na Tsagaita Bude Wuta A Yakin Yeman
Oct 14, 2016 13:37Gwamnatin kasar Britania Zara gabatar da wani shiri na tsagaita bude wuta a yakin da kasar saudia take jagorantar kasashen larabawa a kan kasar yemen.
-
An bukaci shigar Rasha wajen magance rikicin kasar Yemen
Oct 14, 2016 07:33Tsohon Shugaban kasar Yemen ya bukaci shigar Rasha wajen kawo karshen hare-haren wuce gona da iri da kawancen saudiya ke kaiwa kan Al'ummar kasar Yemen.
-
Saudiyya Ta Amince Da Kisan Kiyashin Da Ta Yi A San'a Domin Tsoron Gurfana A Kotun Duniya
Oct 13, 2016 02:08Masarautar iyalan gidan Saud ta amince a hukumance da kisan kiyashin da ta yi a kan daruruwan fararen hula abirnin san'a a na kasar Yemena ranar Asabar da ta gabata.