An Fara Aiki Da Shirin Dakatar Da Bude Wuta A Yemen
Dukkanin bangarori sun fara aiki da shirin dakatar da bude wuta na kwanaki uku a kasar Yemen daga yau Alhamis, wanda za a iya kara tsawon wa'adinsa a lokuta masu zuwa.
Rahotanni daga kasar Yemen sun ce tun daga daren jiya ba a ji hare-haren jiragen yakin masarautar Saudiyya ba kamar yadda aka saba, yayin da sojojin kasar ta Yemen da dakarun sa kai na kabilun larabawa kuma suka dakatar da hare-haren daukar fansa kan 'yan mamaya.
Wanann mataki dai ya zo bayan matsin lambar da kasashen duniya suke yi kan Saudiyya da ta dakatar da hare-haren da take kaiwa kan al'ummar kasar Yemen da sunan yaki da kungiyar Alhuthi, da hakan ya hada har da manyan kawayenta na turai da ke taimaka mata a yakin, musamman Amurka da Birtaniya.
Wannan matsin lamba dai ya zo sakamakon tir da Allawadai da duniya ta yi da masarautar Saudiyya da kuma manyan kasashen turai da ke taimaka mata a yakin na Yemen, bayan kisan kiyashin da masarautar ta Saudiyya ta yi a cikin makon da ya gabata, inda ta kashe fararen hula fiye da 160 a wani wurin zaman ta'aziyya a birnin Sana'a.
kakakin rundunar sojin Yemen Brigadier Sharaf Lukman ya ce a shirye suke su mayar da martani matukar dai 'yan mamaya suka ci gaba da kaddamar da hari kan al'ummar kasar Yemen.