An bukaci shigar Rasha wajen magance rikicin kasar Yemen
Tsohon Shugaban kasar Yemen ya bukaci shigar Rasha wajen kawo karshen hare-haren wuce gona da iri da kawancen saudiya ke kaiwa kan Al'ummar kasar Yemen.
A yayin ganarwarsa da sabon jakadan Rasha a kasar Yemen a jiya Alkhamis, tsohon shugaban kasar Ali Abdal...salih ya bukaci shigar Rasha wajen kawo karshen hare-haren wuce gona da iri da kawancen saudiya gami da Amurka ke kaiwa kan Al'ummar kasar sa.
Abdal..salih ya tabbatar da cewa kasar Rasha babbar kasar tare da hakin kasashen dake bukatar sulhu a Duniya za ta iya samar da wani kudiri a kwamiltin tsaron na MDD da zai dakatar da hare-haren wuce gona da irin da ake kaiwa Al'ummar yemen tare kuma da dage takunkumin da aka sanyawa hanyoyin kasa, Ruwa da sama na kasar.
Tsohon shugaban kasar ta Yemen ya kara da cewa Rasha na iya taimakawa Al'ummar Yemen wajen magance rikicin kasar ta hanyar tattaunawa da juna ba tare da shigar kasashen waje ba.