Pars Today
Hukumar kula da tallafa wa kananan yara ta majalisar dinkin duniya UNICEF ta sanar da dakatar da bayar da tallafin wasu kudade ga al'ummar Yemen, saboda matsalolin da take fuskanta.
Majalisar kare hakkokin bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da sake sabunta aikin kwamitin binciken laifuffukan yaki a kasar Yemen duk kuwa da adawa da hakan da kasar Saudiyya ta yi.
Kungiyar tallafawa yara ta Save the Children ta ce fiye da yara miliyan biyar ne ke fuskantar barazanar yunwa a daidai lokacin da rikicin kasar ke kara kamari kuma farashin kayan abinci ya yi tashin gwaron zabo.
A ci gaba da hare-haren wuce gona da iri da jiragen saman yakin rundunar kawancen masarautar Saudiyya suke kai wa kan kasar Yamen a safiyar yau Litinin sun kashe mutane akalla bakwai.
Wasu mutane a kasar Yemen ba sa da abinci sai ganyen ciyayi saboda matsalolin da yakin da Saudia da kawayenta suka dorawa kasar
Hukumar Abincin ta duniya ta bayyana a jiya juma'a an kai hari akan wasu ma'aiaktanta da cibiyoyin ba da agaji, abin da zai jefa rayuwar mutane miliyan uku da rabi cikin hatsari
Dakarun kasar Aljeriya sun fara kaddamar da wani farmaki da nufin cafke ko halaka jagoran alqaeda a yankin Magrib.
Asusun kula da kananen yara na MDD (UNICEF) ya tabayar da rahoton cewa kasar Yemen ta zamanto jahanama ga kananen yara.
Kakakin kungiyar Ansarullahi ta kasar Yamen ya bayyana furucin da sakataren harkokin wajen kasar Amurka ya yi kan kasar Yamen da cewa: Kokari ne na kara ruruta wutan rikici a kasar da ma yankin gabas ta tsakiya baki daya.
Jiragen yakin kawancen Saudiyya sun kashe mutane 15 da jikkata wasu fiye da 20 a kusa da garin Hudaida dake yammacin kasar Yemen