Sep 29, 2018 05:56 UTC
  • MDD Ta Sake Sabunta Aikin Binciken Yakin Da Saudiyya Ta Kaddamar A Kan Yemen

Majalisar kare hakkokin bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da sake sabunta aikin kwamitin binciken laifuffukan yaki a kasar Yemen duk kuwa da adawa da hakan da kasar Saudiyya ta yi.

Rahotanni sun bayyana cewar Majalisar kare hakkokin bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya da ke da helkwatar a birnin Geneva ta amince da bukatar da kasashen Turai suka gabatar na sake sabunta wa'adin aikin kwamitin binciken da majalisar ta kafa don binciko zargin tafka laifuffukan yaki a kasar Yemen.

Kafin hakan dai Abdrabbuh Mansour Hadi, shugaban kasar Yemen din da yayi murabus sannan ya gudu daga kasar ya bayyanar da rashin amincewarsa da ayyukan wannan kwamitin da kuma sabunta aikinsa na binciko irin laifuffukan yaki da ake zargin gwamnatinsa da kuma gwamnatin Saudiyya sun tabka a kasar ta Yemen.

A baya ma dai 'yan kwamitin binciken sun bayyana damuwarsu dangane da irin halin da al'ummar Yemen din suke ciki biyo bayan ci gaba da hare-haren da gwamnatin Saudiyya da kawayenta suke kai wa Yemen din.

Tags