Mutanen Kasar Yemen Na Cin Ciyawa Don Rayuwa Sanadiyyar Yunwa
(last modified Sun, 16 Sep 2018 19:02:29 GMT )
Sep 16, 2018 19:02 UTC
  • Mutanen Kasar Yemen Na Cin Ciyawa Don Rayuwa Sanadiyyar Yunwa

Wasu mutane a kasar Yemen ba sa da abinci sai ganyen ciyayi saboda matsalolin da yakin da Saudia da kawayenta suka dorawa kasar

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran Associated Press yana cewa mutanen a lardin Aslam arewa maso gabacin kasar Yemen sun dogara da cin ganyen ciyawa wacce ake kira Halas da larabci don rayuwa sanadiyyar rashin abinci da yunwa. 

Wani jami'in kiwon lafiya a yankin Aslam ya ce, garin Hajjah na daga cikin garuruwan da suka fi fama da yunwa a yankin, inda a cikin watan Jenerun shekarar da muke ciki ya zuwa yanzu yawan mutanen da ake kawo masu, wadanda yunwa ta galabaitar da su ya tashi daga 384 zuwa 1,319.

Tun cikin watan Maris na shekara ta 2015 ne gwamnatin kasar Saudia tare da kawayenta na kasashen larabawa suka farwa kasar Yemen da yaki da nufin maida tsohon shugaban kasar Abdu Rabbu Hadi Mansur kan kujerar shugabancin kasar.