UNICEF: Kasar Yemen Ta Zamanto Jahanama Ga Kananen Yara
(last modified Fri, 14 Sep 2018 13:01:40 GMT )
Sep 14, 2018 13:01 UTC
  • UNICEF: Kasar Yemen Ta Zamanto Jahanama Ga Kananen Yara

Asusun kula da kananen yara na MDD (UNICEF) ya tabayar da rahoton cewa kasar Yemen ta zamanto jahanama ga kananen yara.

Cikin wani rahoto da ta fitar, Asusun kula da  kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya  ya ce sama da kananen yara milyan 11 ne ke fama da matsalar karamcin abinci, rashin lafiya da kuma rabuwa da mahalinsu a kasar yemen.

A nata bangare kungiyar farar hula ta kasar Birtaniya mai suna ku ceto kananen yara ta bayyana damuwarta kan yadda kananen yara sama da milyan 4 ke cikin hadarin rasa rayukansu sakamakon matsalar karamcin abinci a kasar ta yemen, sannan ta yi gargadin cewa hare-haren da jiragen yakin kawancen saudiya ke kaiwa tsibirnin Alhudaida na barazana ga rayukan milyoyin rana, musaman ma ganin cewa harin ya nada isar da kayen agaji zuwa gare su.

A ranar 13 ga watan yuni ne kawancen saudiya suka fadada kai hare-harensu a tsibirin Alhudaida da nufin mamaye shi daga Al'ummar kasar

Wannan tsibiri dai shine hanyar daya cilo da masu kai agaji ke amfani da shi wajen isar da taimako zuwa Al'ummar kasar Yemen.