Pars Today
Hukumar kula da abinci ta Majalisar dinkin Duniya FAO ta sanar da cewa yaki ya jefa sama da mutane miliyan 18 cikin matsalar karamcin abinci a kasar Yemen.
Sojojin Yamen da dakarun kungiyar Ansarullahi sun kashe sojojin mamayar Saudiyya masu yawa a sassa daban daban na kasar ta Yamen.
Kakakin Kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Muhamad Abdu-Salam ya ce yakin da kawancen Saudiya ta shiga da kasar ya zo musu da ba zata, kuma za su ci gaba da kashe kudadensu ba tare da cin nasara ba.
Dakarun tsaron Yemen sun samu nasarar hallaka sojojin hayar saudiya da dama a wani farmaki da suka kai sansaninsu na jihar Ta'az dake kudu masu yammacin kasar
Shugaban kungiyar Ansuraullah ta kasar Yemen Abdul-Malik Badruddin Huthi ya bayyan cewa ba zai ki bukatar MDD ta sanya ido a kan lamuran da ke faruwa a birnin Hudaida na bakin ruwa ba amma da sharadin kawancin kasashen da suke yakarsa kasar su dakatar da hare haren da suke kaiwa a kan birnin na Hudaida.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya ce; Kasar tana goyon bayan kiran da wasu fitattaun masana musulmi su ka yi na a kawo karshen yakin kasar Yemen
Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa, Amnesty International, ta zargi Hadaddiyar Daular Larabawa da aikata laifukan yaki a kasar Yemen.
Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya "UNICEF" ya yi Allah Wadai da kashe kananan yara da rundunar kawancen Saudiyya ke yi a kasar Yamen.
Jiragen yakin kawancen saudiya sun kai hari jahar Sa'ada na arewacin kasar, inda suka kashe fararen hula da dama.
Asusun kananen yara na MDD UNICEF ya yi alawadai kan ci gaba da kisan kananen yara a kasar Yemen